Bayan da wasu fursinoni Falasdinawa shida suka tsere daga gidan yarin Jalbu na Isra'ila da ke da tsanannain tsaro, jami'an tsaron Isra'ilan na ci gaba da neman Falasdinawan ruwa a jallo.
Talla
Wadannan fursinoni Falasdinwa dai, sun yi nasarar tserewa daga gidan yarin na Jalbu a Isra'ila, bayan da suka haka rami a karkashin kasa daga bandaki. Dubban Falalsdinawa a birnin Jenin na yankin Falasdinu na ta shagulgulan murna, kan tserewar 'ya'yansu shida daga gidan yarin na Isra'ila na Jalbu da ke dajin kare-kukanka, wanda Isra'ila ke tsare masu zaman daurin rai-da-rai da take ganin suna da matukar hadari.
Wani kusa a kungiyar Jihad al-Islami da 'yan kungiyar tasu shida suka tsere daga gidan yarin, ya ce wannan babbar bushara ce ta 'yantuwar Falalsdinu. Ita ma mahaifiyar guda daga cikin wadanda suka tseren, kira take ga sauran fursinonin da subi sawun danta wajen 'yanta kansu. Shugaban gidajen yarin arewacin Isra'ilan da ke tsaye a gaban ramin da fursinonin suka yi wa bugun da ya ba su damar fita domin tserewa, ya siffanta tserewar da mummunar baraka ga lamarin tsaron gidan yarin.
Rikicin Gabas Ta Tsakiya cikin hotuna
Ruwan rokoki a Tel Aviv, rusau a Gaza - Rikici tsakanin Israila da Falasdinawa na kara yin kamari a 'yan kwanakin nan. Sai dai kamar kullum farar hula daga bangarorin biyu sune ke shan wuya.
Hoto: Mahmud Hams/AFP/Getty Images
Israila na kai harin ramuwar gayya
Barnar ba ta kare ba. Jiragen yakin Israila na luguden bama bamai a kudancin Gaza inda ta ke kai hari kan kungiyar Falasdinawa ta Hamas.
Hoto: Said Khatib/AFP/Getty Images
Isra'ila ta kira dakarun wucin gadi
Rundunar sojojin Israila na yin gangamin dakaru da tankokin yaki a kan iyaka da zirin Gaza lamarin da ke tunato da abin da ya wakana a yakin 2008 da 2009 da kuma 2014.
Hoto: Amir Cohen/REUTERS
Hudowar rana
Hayaki ya turnuke sararin samaniya a wannan Laraba a Khan Younis a yankin zirin Gaza. Tun a farkon mako rikici tsakanin Israila da Falasdinawa ya barke a bainar jama'a.
Hoto: Youssef Massoud/AFP/Getty Images
Neman tsira da rayuwa
A birnin Gaza, wadannan falasdinawan sun guje wa farmakin Israila a ranar Talata. Akalla ‘yan Israila takwas suka rasu yayin da ma’aikatar lafiya ta Falasdinawa ta ruwaito cewa akalla mutane 109 suka rasu run daga ranar Litinin.
Hoto: Mahmud Hams/AFP/Getty Images
Rusau a birnin Gaza
Israila ta ce ta kai hari kan gidaje kamar wannan a birnin Gaza, wanda ke dauke da ofisoshi na ‘yan kungiyoyin ‘yan bindiga ko kuma inda shugabannin tsagerun ‘yan Hamas ke zaune.
Hoto: Suhaib Salem/REUTERS
Harin rokoki a Tel Aviv
Kungiyar Hamas da ke mulki a zirin Gaza ta harba rokoki cikin Tel Aviv a daren ranar Laraba. Na’urorin kakkabo makamai masu linzami na Isrila suna bada kariya ga birnin tare da lalatawa ko kuma sake tankada makaman masu linzami zuwa sama yadda ba za su yi wani lahani mai yawa ba.
Hoto: AnAs Baba/AFP/Getty Images
Jira cikin kaguwa
Sai dai kuma na’urar kakkabo makaman masu linzami da ake kira “Garkuwar karfe“ ba ta samar da kariya dari bisa dari. Idan aka busa sarewa dukkan ‘yan Israila sai su bazama neman mafaka cikin gaggawa. Ko da kuwa da karfe uku ne na dare kamar wannan safiyar a nan.
Hoto: Gideon Marcowicz/AFP/Getty Images
Har yanzu akwai hadari
Ko da za a kakkabo rokokin Falasdinawa, baraguzai da ke fadowa suna da hadari. An lalata wani gida a wannan yankin Yahudawa da ke arewa da babban firin jirgin saman Israila. A cewar sojojin Israila Falasdinawa sun harba rokoki fiye da 1000 tun daga ranar Litinin.
Hoto: Gil Cohen-Magen/AFP/Getty Images
Hannu a Ka
Duk wanda bai iya samun mafaka akan lokaci ba, kan yi kokari bakin iyawarsa yadda zai tsira kamar wadannan mutanen a yankin Ashkelon da ke tazarar kilomita 10 daga arewacin zirin Gaza.
Hoto: Jack Guez/AFP/Getty Images
Duwatsu da gwangwanayen hayaki mai sa hawaye
A ‘yan kwanakin baya bayan nan ana ta samun gagarumar zanga zanga tsakanin Falasdinawa da jami’an tsaron Israila a birane da dama, kamar nan birnin Hebron a yankin da Isriila ta mamaye a gabar yamma. Masu zanga zanga na ta jifa da duwatsu da sauran abubuwa.
Hoto: Hazem Bader/AFP/Getty Images
Hotuna 101 | 10
Gidan talabijin na Isra'ilan dai, ya nuna hotunan karshe da kyamarar gidan yarin ta dauka na fursinonin shida suna kai wa suna komawa a cikin gidan yarin, kafin su yi batan dabo. Ana zaton fursinonin Falasdinun sun yi anfani da cokulan cin abincin da ake ba su ne, wajen haka ramin mai tsayin mita 25, kasancewa ba a barin masu ziyarar su shiga da ko da tsinke ne. 'Yar sandar Isra'ilan da ke kan hasumiyar duba farfajiya da wajen gidan yarin dai, ta fadawa masu bincike cewa gyangyadi ya yi ta kwasheta a daren da fursinonin suka tsere. Idan ana iya tunawa dai, a shekarar 1986 ne wasu fursinonin Falasdinawa suka tsere daga gidan yarin Zirin Gaza, lamarin da ya zama masomar tilastawa Isra'ilan ficewa daga Zirin na Gaza.