1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IsraIla ta kara dakaru a Falasdinu

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 9, 2021

Bayan tserewar wasu fursinoni Falasdinawa shida daga gidan kurkuku mafi tsaro a Isra'ila, a yanzu haka Isra'ilan ta kara yawan sojojinta da ke jibge a Gabar Yamma da Kogin Jordan.

Palästinensische Häftlinge flüchten aus Gefängnis in Israel
Dakarun Isra'ila, na ci gaba da farautar fursinonin nan Falasdinawa da suka tsereHoto: Gil Eliyahu/JINI via Xinhua/picture alliance

Rahotanni na nunar da cewa, sojojin da aka jibge sun hadar da babbar rundunar sojoji da dakarun sirri da kuma jiragen yaki. A wani mataki na binciko fursnonin da suka tsere daga gidan kason, Isra'ilan ta kuma kara yawan jami'an 'yan sandanta da na leken asiri a Falasdinun, baya ga kara yawan yankunan Falasdinawa da tai wa kawanya. A yanzu haka dai, jami'an tsaron na Isra'ila za su ci gaba da yin kawanya a yankunan Falasdinawan har zuwa Jumma'ar wannan makon.