Isra'ila na ci gaba da rushe gidaje a Gaza
September 15, 2025
Akalla gine-gine 30 ne sojojin Isra'ila suka lalata a Zirin a ranar Lahadi, lamarin da ya tilastawa dubban Falasdinawa barin gidajensu.
Marco Rubio wanda ya Isa Tel Aviv da zummar tattauna makomar yakin Isra'ila a Gaza, ya bayyana bukatar Washington na nema sakin wadanda mayakan Hamas ke ci gaba da garkuwa da su da kuma batun sake gina Gaza.
Duk dai a kan wannna batu na rikicin Isra'ila da Hamas.
Harin ranar 9 ga Satumba, wanda Isra'ila ta kai a Qatar da zummar samun jagororin Hamas, Hamas ta ce ya kashe biyar daga cikin mambobin amma bai taba shugabanninta ba, harin yasa ana aza ayar tambaya a kan kawancen dake tsakanin Amurka da Qatar da ma sauran kasashen Larabawa, wanda ake ganin ya dagula al'amura.
Kasashen Larabawa za su sake yin nazari a kan yarjejeniyar Abraham wacce suka kula da Isra'ila shekaru biyar da suka gabata.
Karin Bayani: Isra'ila ta dau alhakin kai wa jagororin Hamas a birnin Doha na Katar