1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Daruruwan Falasdinawa na tserewa daga Khan Younes

Abdourahamane Hassane
August 11, 2024

Daruruwan Falasdinawa na tserewa daga unguwannin Khan Younes da ke kudancin Gaza, inda sojojin Isra'ila ke shirin kai sabbin hare-hare,

Hoto: Rizek Abdeljawad/Xinhua/IMAGO

 Hakan ya biyo bayan kwana guda bayan wani samame da suka kai a kan wata makarantar da ake ganin yana daya daga cikin hari mafi muni tun bayan fara yakin tsakanin Israila da Hamas. Tun farko Isra'ila ta yi kira ga fararen hula da su fice daga yankin al-Jalaa , wanda a baya aka ayyana shi a matsayin yankin jin kai.Sojojin Isra'ilar sun yi ikirarin cewa Hamas ta girke kayayyakin aikin ta'addanci a wannan yanki kuma tana shirin kaddamar  da farmaki.