Amirka ta gargadi Isra'ila game da yunkurin kai hari Iran
July 24, 2015Kerry ya bayyana haka ne a wani shiri mai taken "Today" da tashar talabijin ta NBC ke yadawa, inda ya ce duk wani hari da Isra'ilan za ta kai na soja ko kuma na kafar Internet da ake kira da Cyber Attack kuskure ne za ta tafka gagarumi wanda kuma zai haifar mata da yin da na sani mara amfani. Ya kara da cewa illar kuskuren ba wai a kan Isra'ilan kawai za ta tsaya ba har ma da yankin Gabas ta Tsakiya baki daya. Tun dai bayan da aka cimma yarjejeniya kan batun makamashin nukiliyar Iran din tsakanin Iran da manyan kasashe shida masu fada aji a duniya, Isra'ila ke ci gaba da yin kumfar baka da kuma nuna adawarta da matsayar da aka cimma din inda ta sha alwashin daukar matakin da take ganin ya dace a kan Iran din ba tare da yin shawara da kowa ba.