Siyasar Isra'ila ta dauki sabon salo
March 17, 2020Benny Gantz mai shekaru 60 a duniya yana da sassaucin ra'ayi matuka duk da cewa yana goyon bayan galibin siyasar Benjamin Netanyahu ta yin babakere a yankunan Falasdinawa da fifita bukatun Yahudawa kan sauran 'yan kasar Isra'ila.
Duk da yake yana ganin cewa zakewa wajen hana Falasdinawa hakkokinsu da badakalar da shuwagabanni ke yi da kudaden al'umma su suka fi zama barazana ga dorewar Isra'ila, don haka dole ya dukufa wajen ganin ya dinke barakar cikin gida kafin fuskantar sauran kalubale.
Benny Gantz ya ce zai yi iya kokarinsa na kafa gwamnatin da za ta kunshi dukkanin bangarorin siyasar kasar ta Isra'ila.
"Zan kare Yahudawa 'yan kama wuri zauna a ko ina suke, kamar yadda zan kare Larabawan da ke Isra'ila. Babu ta yadda za mu iya kare kanmu da samun dorewar kasarmu muddin ba mu bai wa kowane dan kasa hakkinsa ba. Cutar Corona da ke barazana ga 'yan Isra'ila abin kunya ne da ke nuna gazawar gwamnati da jagororinta 'yan cuwa-cuwa ne."
Duk da cewa jam'iyyun Larabawan Isra'ila sun goyi bayan Benny Gantz da kuri'ar da suka kada sun gindaya sharudda na shiga gwamnatin da Gantz din ke shirn kafawa a gaba. A nasu bangaren Falasdinawan da ke zaune a yankunan da Isra'ila ke mamaya na ganin cewa har yanzu duk gautar ja ce, suna masu cewa da Benny Gantz da Benjamin Netanyahu duk dan Jumma ne da dan Jummai domin mulkinsu irin na wariya da kama karya ne.