1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta ƙaddamar da farmaki a Gaza

Usman ShehuMarch 10, 2012

Wani sabon tashin hankali tsakanin Isra'ila da Falasdinawa ya hallaka mutane da yawa a zirin Gaza

Palestinians inspect the damage to a Islamic Jihad sports club following an Israeli air strike in Beit Lahiya, northern Gaza Strip, early Thursday, Aug. 25, 2011. Israeli aircraft targeted an Islamic Jihad sports club early Thursday, killing two Palestinians. Palestinian militants fired rocket barrages that wounded an Israeli baby Wednesday, and Israel retaliated with airstrikes that killed four Gaza fighters, Gaza officials said. (Foto:Adel Hana/AP/dapd)
Wasu gidajen a Gaza da farmakin Isra'ila ya rusaHoto: dapd

Isra'ila na ci gaba da luguden wata kan yankin Gaza inda ta hallaka mutane aƙalla mutane 14. Wannan kai farmakin Isra'ila wanda aka fara tun daren jiya ya biyo bayan farmakin rokoki daga mayagan gwagwarmaya dake Gaza. Abinda ya fi tunzura lamarin shine kisan wani jagoran mayaƙan kungiyar PRC, inda ƙungiyar dama Hamas suka yi alƙawarin daukar fansa. Kawo yanzu ana ci gaba da kai farmakin jiragen sama daga bangaren Isra'ila, yayinda su kuwa mayaƙan Falasdinu aka ce sun cilla aƙalla rokoki 90 cikin Isra'ila, inda suka raunata mutane hudu.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Abdullahi Tanko Bala