1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta amince da shirin tsagaita wuta

Suleiman Babayo AH
November 26, 2024

Firamnistan Isra'ila ya gabatar da jawabi game da amincewa da shirin tsagaita wuta da mayakan Hezbollah na Lebanon

Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila
Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ilaHoto: Pool European Pressphoto Agency/AP/dpa/picture alliance

Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila ya gabatar da jawabin amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnatinsa da mayakan kungiyar Hezbollah na Lebanon. Firaminstan ya tabbatar da haka bayan kammala ganawa da jiga-jigan gwamnatinsa. Tun farko manyan jami'an gwamnatin Lebanon sun nuna fata kan samun amincewa da wannan yarjejeniyar tsagaita wutar.

Karin Bayani: Isra'ila ta kai wani sabon hari a tsakiyar birnin Beirut na Lebanon

Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da mayakan Hezbollah, a wannan Talata dakarun Isra'ila sun kai hare-hare ta sama birnin Beirut fadar gwamnatin Lebanon, wuraren da ake dauka tungar mayakan na Hezbollah da ke samun goyon bayan kasar Iran.