Isra'ila ta bai wa Yahudawa fifiko
July 19, 2018Talla
Dokar ta samu amincewar 'yan majalisu 62 yayin 'yan majalisu 55 suka yi ki amincewa da kudurin, sai dai 'yan majalisu da ke wakiltar Larabawa a majalisar sun yi Allah wadai da matakin tare da nuna fargabar yunkurin murkushe 'yancin dimukuradiyya. Firaministan Isra'aila Benjamin Natanyahu ya jinjinya wa 'yan majalisar Isra'ila da suka yi fafatukar tabbatar da doka a mastayin yunkurin da ya shiga tarihin kasar.