1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra’ila ta ayyana birnin Gaza a matsayin “fagen daga''

August 29, 2025

Sojojin Isra’ila sun ayyana birnin Gaza a matsayin “fagen daga mai hatsari”, a gabanin wani sabon farmaki da suke shirin kaiwa don kwace birnin mafi girma a yankin Falasdinu.

Hoto: JACK GUEZ/AFP/Getty Images

A wata sanarwa da ta fitar a wannan Jumma'a, rundunar sojin Isra'ila ta ce daga yanzu birnin Gaza ya zama yanki na fada mai hatsari, kuma za ta daina tsagaita kai hare-hare da take yi a kowacce rana domin ba da damar rarraba kayan agaji. Amma duk da haka, sojojin na Isra'ila ba su bayar da umurni ga jama'a su bar birnin Gaza nan take ba. Sai dai mai magana da yawun rundunar a harshen Larabci, Avichay Adraee, ya ce sun riga sun fara shirye-shiryen farmaki da matakan farko na kai hari kan birnin, inda yanzu haka sojojinsu ke aiki ba ji-ba-gani a bayan birnin Gaza.

Hakan na zuwa ne a yayin da Isra'ila ke fuskantar matsin lamba daga cikin gida da waje domin ta kawo karshen farmakin da take yi a Gaza, inda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa yunwa ta barke a hukumance.