Isra'ila ta ba da sa'o'i 24 don kwashe mazauna Gaza
October 13, 2023![Tankokin yakin Isra'ila](https://static.dw.com/image/67084655_800.webp)
Wannan na nuni da shirin tabbatar da alwashin da Isra'ila ta dauka na abkawa Zirin Gaza domin fatattakar 'yan kungiyar Hamas da ta kira a matsayin 'yan ta'adda tare kuma da kwato mutanen da ta yi karkuwa da su lokacin da aka fara rikicin.
Karin bayani: Kokarin sako Isra'ilawa daga hannun Hamas
Sai dai a lokacin da ya ke sanar da wannan umurni na Isra'ila, kakakin sakataren Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric ya bukaci Tel-Aviv da ta soke wannan mataki yana mai gargadin kadda bayan kashe-kashen da aka yi a kasa da mako guda, yankin ya sake fadawa cikin munmunan yanayi.
Karin bayani: Isra'ila ta yi wa yankin Gaza kawanya
Daga nasa waje jakadan Isra'ila a Majalisar Dinkin Duniya Gilad Erdan tir ya yi da wannan martani da majalisar ta yi yana mai zarginta da rufe idanuwa a lokacin da ya ce kungiyar Hamas ke cefano makamai tana boyewa a Zirin na Gaza.
A wannan Jumma'a (13.10.2023) kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai yi taron gaggawa a asirce kan wannan sabon rikici na Isra'ila da kungiyar Hamas yayin da ake daf da cika mako guda da barkewarsa.