Isra'ila ta bukaci hanzarta warware rikicin Siriya
March 12, 2013Shugaban kasar Isra'ila Shimon Peres ya jaddada kira ga dakarun kungiyar kasashen Larabawa da ta tsoma baki a cikin rikicin da ke ci gaba da wanzuwa a kasar Siriya domin ceto al'ummar kasar daga matsananciyar rayuwar da suka tsinci kansu a ciki. Shugaban ya fadi hakan ne a jawabin da ya gabatar ga taron majalisar dokokin kasashen Turai a wannan Talatar. Jawabin dai shi ne karo na farko da wani shugaban kasar Isra'ila ya yi a gaban majalisar dokokin tarayyar Turai tun cikin kimanin shekaru 30 da suka gabata.
Peres ya kara da cewa yakamata Majalisar Dinkin Duniya ta tallafawa kungiyar kasashen larabawa domin gano bakin zaren warware halin da ake ciki a kasar ta Syria muddin dai ana son cimma burin da aka sa a gaba na hana yaduwar makaman nukiliya a hannun bata-gari da ke cikin kasashen larabawa. Kazalika - a cewar shugaban na Isra'ila ba za a iya shawo an rikicin ba in har za a ci gaba da zubawa shugaba Bashar al-Assad ido yana kashe al'ummar sa.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe