SiyasaGabas ta Tsakiya
Isra’ila Ta Kashe Sabon Shugaban Rundunar Hamas a Gaza
May 27, 2026
Talla
Akalla Falasdinawa guda uku aka kashe sannan gommai sun ji rauni a gagarumin harin wanda ya fada kan wani gida a daya daga cikin manyan kasuwanni a zirin Gaza, kamar yadda shaidu suka bayyana.
Sojojin Isra'ila sun ce an kai harin ne a kan gine-ginen da ke zama mafakar shugaban reshen kungiyar bayan da aka bibiye shi na tsawon wata da watanni kafin ya fada hannu.
Harin da ya kashe Odeh shi ne hari mafi muni da Isra'ila ta kai kan Gaza duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da ta cimma da Hamas wadda ta fara aiki a Oktoba, amma harnyazu Hamas ba ta ce komai ba kan lamarin.