1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta ce tana taimaka wa dakarun MDD a Siriya

December 7, 2024

Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarunta na taimakawa jami'an Majalisar Dinkin Duniya a yankin Tuddan Golan da ke karkashin ikon Siriya domin dakile hare-haren 'yan tawaye.

Hoto: Nicolas Economou/NurPhoto/picture alliance

Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarunta na taimakawa jami'an Majalisar Dinkin Duniya a yankin Tuddan Golan, domin dakile hare-haren mutanen da ke dauke da makamai. A cikin sanarwar da rundunar ta fitar, ta ce wasu 'yan bindiga sun kai hari a kusa da offishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Hader a kasar ta Siriya.

Karin bayani: Siriyar: 'Yan tawayen HTS na gallazawa farar hula

Tun da fari, 'yan tawayen Siriya sun kwace iko da Lardin Quneitra da ke da nisan kilomita 12 zuwa kudancin Hader, a cewar kungiyar kare hakkin dan Adam ta Siriya da ke da mazauni a Birtaniya. Rundunar sojin Isra'ila na cewa, ta karfafa karfin dakarunta a yankun da Isra'ila ta mamaye a Golan kana ta gudanar da atisayen soji domin shirin kar ta kwana sakamakon halin da ake ciki.