1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta ce tsagaita yakin Iran ba ta shafi Lebanon ba

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 8, 2026

Isra'ila ta ce wajibi Iran ta bude mashigin Hormuz ta dakatar da kai hari ga Amurka da Isra'ila da kawayen Amurka a Gulf

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanjahu
Firaministan Isra'ila Benjamin NetanjahuHoto: Ronen Zvulun/REUTERS

Isra'ila ta nuna goyon bayanta ga matakin shugaban Amurka Donald Trump, na dakatar da yakin Iran har na tsawon makonni biyu, to sai dai ta ce yarjejeniyar tsagaita wutar ba ta shafi Lebanon ba.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya ce wajibi ne Iran ta bude mashigin Hormuz ta kuma dakatar da kai hari ga Amurka da Isra'ila da kuma kawayen Amurka na yankin Gulf.

Karin bayani: 'Hare-hare kan ababen more rayuwa laifin yaki ne' - MDD

Sanarwar da ofishin firaministan ya fitar, ta jaddada goyon Isra'ila kan matakin Amurka, domin kwance damarar Iran ta mallakar makamin nukiliya, wanda ke zama barazana ga Amurka da Isra'ila da kuma makwabtan kasashen Larabawa.

Tuni firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ya ce birnin Islamabad na kasar zai karbi bakuncin wakilan Amurka da Iran a ranar Juma'a, 10 ga Afirilu, fara tattaunawar daddale yarjejeniyar dakatar da yakin Gabas ta Tsakiya.

Karin bayani:Isra'ila ta dakile hari daga 'yan tawayen Houthi na Yemen 

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X da safiyar Laraba, Mr Sharif, wanda shi ne babban mai shiga tsakani don cimma wannan masalaha, ya jinjinawa jagororin kasashen biyu da suka martaba gayyatarsa, ta neman cimma sulhu.

Ya kara da cewa yarjejeniyar ta fara aiki nan take, kuma ta hada da rikicin Isra'ila da Lebanon, ko da yake Isra'ila ta ki aminta da hakan. 

Sauran kasashen da suka taka gagarumar rawa wajen samun wannan ci gaba, sun hada da Turkiyya da Masar da kuma China.