1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta daina buɗe wuta a zirin Gaza

Englisch-redMarch 13, 2012

Isra'ila da palesɗinawa sun cimma yarjejeniyar sulhunta rikicin da ya ɓarke bayan kashe wani mai fafutikar samar wa Palesɗinu da 'yancin cin gashin kanta.

Palestinian protesters hold flags as they stand on a vehicle partly covered by a banner depicting jailed Islamic Jihad leader Khader Adnan, during a weekly demonstration against the controversial Israeli barrier, in the West Bank village of Bilin near Ramallah February 17, 2012. Several thousand Palestinians rallied in Gaza and the West Bank on Friday in support of Adnan, who is on the 62nd day of a hunger strike to protest his detention by Israel. REUTERS/Ammar Awad (WEST BANK - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Kasahe Khader Adnad ya jawo rigima a zirin Gaza.Hoto: Reuters

ƙasar Masar ta yi nasarar sulhunta rikicin da ya ɓarke tun kwanaki huɗun da suka gabata a zirin Gaza tsakanin Isra'ila da kuma Palesɗinawa. Tashar telebijin mallakar gwamnatin ta Masar ta bayyana cewar ɓangarorin biyu sun amince su ajiye makamai tun da misalin ƙarfe ɗayan dare na wannan talatar.

A halin yanzu dai ba a jin aman bindigogi a Zirin na Gaza da kuma kudancin ƙasar Isra'ila. Dama dai palesdinawan sun yi alƙawarin daina harba wa bani yahudu rokoki. yayin da ita kuma Isra'ila ta ce za ta daina amfani da jiragen saman yaƙinta domin ci-gaba da kai farmaki akan Falasɗinawa a Zirin Gaza.

Tun da farko dai, ƙungiyar Hamas dake jan ragamar iko a Zirin na Gaza ta yi kira ga sauran ƙasashen yankin da su tsoma baki wajen kawo ƙarshen rikicin, wanda ya ɓarke bayan mutuwar wani shugaban gwagwarmayar ƙwato wa palesɗinawa 'yancinsu,a wani harin da jiragen saman yaƙin Isra'ila suka kai a Zirin Gaza.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu