1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila: Fara kai hare kan gine-ginen Al-Qard Al-Hassan

October 21, 2024

Daruruwan mazauna Beirut sun fara tsere wa jim kadan kafin a fara jiyo karar fashewar bama-bamai, yayin da Isra'ila ta fara kai farmaki kan gine-ginen bankin Al-Qard Al-Hassan.

Isra'ila ta fara kai hare kan gine-ginen bankin Al-Qard Al-Hassan
Isra'ila ta fara kai hare kan gine-ginen bankin Al-Qard Al-Hassan Hoto: Hussein Malla/AP Photo/picture alliance

Mazauna yankin da suka nemi a saka sunayensu sun ce wani gini ya rushe sakamakon harin a garin Chiyah da ke kusa da kudancin Beirut, sai dai ba a samu asarar rayuka ba sakamakon tsere wa da mazauna garin suka yi gabanin harin.

Tun da fari, a sakon da ya wallafa a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter a baya, kakakin rundunar sojin Isra'ila ya ce, Isra'ila za ta fara kai hare-hare kan gine-gine mallakin bankin Al-Qard Al-Hassan, bankin da Amirka ta ce Hezbollah na amfani da shi wajen gudanar da harkokin kudinta.

Bankin na da rassa kimanin guda 30 a Lebonan ciki har da 15 da ke a cikin Beirut da kewaye. Sai dai Kungiyar Hezbollah da gwamnatin Lebanon ba su ce uffan ba kan wannan matakin na Isra'ila.