An janye dakaru Isra'ila
July 5, 2023Talla
Gwamnatin kasar Isra'ila ta janye dakaru daga yankin gabar yamma da kogin Jodan inda tsageru masu dauke da makamai suka yi kaka-gida, abin da ya kawo karshen matakin soja na tsawon kwanaki biyu da ya yi sanadiyar mutuwar Falasdinawa kimanin 12.
Sojojin sun bayyana samun galaba wajen yin ta'adi kan tsagerun yayin samame a sansanin 'yan gudun hijira na Jenin. Akwai sojan Isra'ila daya da ya rasa ransa lokacin artabun.
Gabanin janye dakarun Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila ya sha alwashin cewa za a sake amfanin da sojojin muddun aka sake samun barazana daga kungiyoyin tsageru masu dauke da makamai na Falasdinu.