Sabon farmakin Isra'ila kan Gaza
September 16, 2025
Dakarun Isra'ila sun kaddamar da sabon farmaki a yankin zirin Gaza na Falasdinu, inda dakarun ke cewa za su zurfafafa dannawa cikin yankin domin tunkarar mayakan kungiyar Hamas kimanin 3,000. Akwai masu tababa da nuna dari-dari da haka a cikin Isra'ila kan makomar 'yan Isra'ila da aka yi garkuwa da su a cikin yankin na Falasdinu.
Rkiicin ya fadada
Farmaki na zuwa lokacin da kasashen Turai ke barazanar takunkumin kan gwamnatin Isra'ila.
Shi ma sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce matakin na Isra'ila kan yankin na Falasdinu ya saba ka'idojin siyasa da dokokin duniya.
Sannan babban jami'in na majalisar Dinkin Duniya ya ce yana shirye da ganawa da Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila da Shugaba Donald Trump na Amurka, lokacin taron majalisra a mako mai zuwa.