1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta kai hare-hare a kudancin Labanan

January 10, 2024

Dakarun Isra'ila sun kai wasu hare-hare a yankunan da mayakan Hezbollah ke a cikin su a kudancin kasar Labanan, a daidai lokacin da rikici ke kara rincabewa a iyakar kasashen.

Yankin da Isra'ila ta kai wa hare-hare a Labanan
Yankin Naqura da Isra'ila ta kai wa hare-hare a LabananHoto: Jalaa Marey/AFP

Dakarun na Isra'ila sun tabbatar da da kai harin ne a sansanin soji da ke Naqoura, bayan harba wasu rokoki da aka yi daga yankin da  kuma ya fada cikin Isra'ilar.

A cewar sojojin na Isra'ila dai, sun afka wa mazaunin 'yan ta'adda ne, yayin kuma da ma'aikatar tsaron kasar Labanan ke cewa hare-haren ramuwar gayya daga Isra'ilar a wannan Laraba, sun fada ne kan wasu kauyuka da ke iyakar kasashen biyu.

A wani labarin kuma, Ma'aikatar lafiya da kungiyar Hamas da ke karkashin Hamas a Zirin Gaza, adadin wadanda suka mutu a cikin sa'o'i 24 da suka gabata sakamakon luguden wuta daga Isra'ila sun kai 147.

Tun bayan fara yaki tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas dai, yanzu jami'an fararen hula dubu 23 da 357 suka rasa rayukansu 

Adadin kuma wadanda suka jikkata, su ne mutum dubu 59,410.