1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Israila ta kai hari da makamai masu linzami a zirin Gaza

Hauwa Abubakar AjejeSeptember 26, 2005

Saoi kadan bayan Hamas ta sanarda dakatar da bude wuta akan Palasdinu,sojojin Israilan su kai farmaki birnin Gaza da Khan Yunis

Yan kungiyar Hamas
Yan kungiyar HamasHoto: AP

Saoi kadan bayan kungiyar Hamas ta bada sanarwar tsagaita bude wuta kan Israila daga Zirin Gaza,sai ga shi sojin Israila sun kai hare hare da jirage a birnin Gaza da Khan Yunis.

Babban jagoran kungiyar Hamas,Mahmoud al-Zahar ya sanarda wannan tsagaita wuta jim kadan bayan sojojin Israila sun kashe wani shugaban kungiyar Islamic Jihad.

Yace kungiyar Hamas zata bi yarjejeniyar da aka cimmawa a watan maris daya gabata,ya kara da cewa wannan shawara da Hamas ta yanke zai tabbatar da tsaron Palasdinawa a Zirin Gaza.

Harin na yau sojin Israilan sunce su kai ne akan abinda suka kira hanyoyin da yan taadda suke bi bi suna kai hare hare cikin Israila,da kuma wuraren da suka ce ana boye makamai a yankin Khan Yunis.

Wani wanda ya ganewa idanunsa yace wata mata ta samu rauni a harin na yau.

Amma yayinda Kungiyar Hamas mafi karfi cikin kungiyoyi masu kishin addinin Islama take wannan alkawari,sauran kungiyoyin Islama a yankin basu goyi bayanta ba.

Domin kuwa saoi kadan bayan sanarwar da al-Zahar yayi na dakatar da bude wutar,sai ga shi wasu yan bindiga na kungiyoyi biyu da suka hada da shahidan al-aqsa na kungiyar Fatah ta shugaba Mahmud Abbas,sun harba roket roket zuwa cikin Israila.

Sai dai duk da yanke shawarar da kungiyar Hamas tayi na tsagaita wuta,wani jamiin gwamnatin Israila wanda bai yarda an baiyana sunansa ba,yace dole Hamas din ta nuna sadaukarwa akan wannan alkawari da ta dauka,inda yace muddin dai yan kungiyar Hamas suna dauke da makamai kuma suna kan akidarsu ta neman lalata Israila,to fa zata ci gaba da kasancewa makiyar Israila kuma ta hakan zata maida martani akanta.

Rikici na baya bayan nan ya barke ne tun ranar jumaa a yayinda wasu mutane 16 suka rasa rayukansu,a lokacinda bam ya fashe a cikin gangamin yan kungiyar Hamas din a birnin Gaza.

Kungiyar ta Hamas ta dora laifin wannan hari akan Israila,a martani da suka yi yan bindiga sun harba roket roket akalla 40 zuwa cikin Israila.

Kodayake Isarailan, ta karyata cewa ita ta kai wannan hari,hakazalika hukumar Palsadinawa tace da alamun cewa nakiyoyi day an kungiyar Hamas suke dauke da shi ne suka fashe a lokacin gangamin har suka yi sanadiyar mutuwar wadanan mutane.

Kungiyar ta Hamas sai kara samun goyon baya take yi daga jamaar Plasdinawa a zirin Gaza musamman bayan janyewar yahudawa daga yankin, da kuma gwagwarmaya na shekaru 4 da rabi da take ci gaba da yi bisa mamayar da Israila tayiwa yankunan Plasadinawa.

A halin yanzu dai kungiyar Hamas ta shirya kalubalantar kungiyar Fatah ta Shugaba Mahmud Abbas,a zaben majalisar dokoki da zaa gudanar karo na farko a shekara mai zuwa.