Isra'ila ta kai hari Gaza
February 18, 2018Talla
Jiragen yakin Isra'ila sun kai hare-hare kan yankin zirin Gaza, bayan raunin da wasu sojojin kasar suka ji sakamakon tashin bom a ranar Asabar a yankin Falasdinawa. Ma'aikatar tsaron Isra'ilar ta ce ta afka wa akalla sansanonin shida da ke yankin na Falasdinawa, saboda amannar da suka cewar falasdinawan sun dasa boma-boman da gangan a Juma'ar da ta gabata, kuma suka ajiye tutarsu.
Kamfanin dillancin labaran Falsdinu Wafa, ya ce wasu makamai masu linzami da Isra'aila ta harba, sun lalata gidaje a wurare uku a Gaza. Lamura dai sun kara tabarbarewa tsakanin Isra'ila da Falasdinu ne tun cikin watan Disamba, lokacin da Shugaban Amirka Donald Trump ya bayyana amincewa da birnin Kudus a matsayin fadar gwamnatin Isra'ila.