Isra'ila ta sake kai hari zirin Gaza
June 16, 2021Talla
A karon farko tun bayan kawo karshen rikicin kwanki 11 a zirin Gaza, wanda ya yi sanadiyar mutuwar Faladsinawa sama da 200, Isra'ila ta kaddamar da hare-haren ramuwar gayya zuwa zirin gaza, bayan da kungiyar Hamas ta harba balam-balam masu fashewa da suka haddasa gobara a wasu yankunan Isra'ilar.
Matakin ya biyo bayan wani tattaki da Yahudawa masi kishin kasa su ka yi a gabashin birnin Qudus a ranar Talata, wanda ya haifar da kakkausar suka daga bangaren Hamas wacce ke iko da Gaza a hukumance.