1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta kai jerin farmaki a Yamen

Usman Shehu Usman
December 19, 2024

Bayan hare-haren da mayakan Houthi ke kai a Isra'ila tun fara yakin Gaza, a wannan Alhamis Isra'ila ta kaddamar da farmakin jiragen yaki a sassan kasar Yamen kama daga tashar jiragen ruwa izuwa Sana'a babban birnin kasar

Jemen Sanaa 2024 | Zerstörung in Kraftwerk nach israelischem Luftangriff
Hoto: Khaled Abdullah/REUTERS

Rundunar sojan Isra'ila ta ce ta kai gagarumin farmakin da jiragen yaki ciki har da jirage marasa matuka da sauran kayan yaki, duk an turasu a yankin kasar Yamen mai nisan kilo mita 1,700 daga Isra'ila. Hare-haren Isra'ilan dai sun ragargaza tashoshin makamashi a Sana'an babban birnin kasar ta Yamen. Wata sanarwar da aka wallafa ta ce Benjamin Netanyahu firimiyan Isra'ila, ya dau wadannan matakai kai hari cikin Yamen ne, a martani kan jerin hare-haren da mayakan Houthi suka yi ta kai wa Isra'ila, inda ko a wannan Alhamis wani harin mayakan Houthi da ya rutsa da wata makaranta a cikin Isra'ila. Tun fara yakin Gaza ne dai mayakan Houthi ke kai hare-hare wa Isra'ila a matsayin gudumawa ga Palastinawan Gaza wadanda Isra'ila ke kai wa farmaki tun bayan harin bakwai ga watan Oktoba.