1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta kai munanan hare-hare a tsakiyar birnin Beirut

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim MAB
October 3, 2024

Halaka sojojinta takwas da aka yi a kusa da iyakar Lebanon bayan da iran ta harba makamai ne ya sa Isra'ila ta mayar da martani a babban birnin kasar wato Beirut.

Hayaki na turnuke birnin Beirut idan Isra'ila ta kai farmaki
Hayaki na turnuke birnin Beirut idan Isra'ila ta kai farmakiHoto: Amr Abdallah Dalsh/REUTERS

Dakarun sojin Isra'ila sun kai munanan hare-hare a tsakiyar Beirut babban birnin kasar Lebanon, biyo bayan halaka sojojinta takwas da aka ranar Laraba a kusa da iyakar Lebanon, a daidai lokacin da zaman dardar ke karuwa kan shirinta na kai harin ramuwar gayya ga babbar abokiyar gabarta Iran. Isra'ilar ta yi ruwan bama-bamai ne a birnin Beirut, bayan da iran ta harba ma ta makamai masu linzami kusan 200, inda firministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ke cewa Iran za ta dandana kudarta bisa kuskuren da ta aikata.

Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta ce a cikin tsawon sa'o'i 24, harin Isra'ila ya halaka mutane 46, tare da jikkata wasu 85. Kuma daga fara kai wannan farmaki zuwa yanzu mutane 1,928 ne suka mutu a Lebanon.

Karin bayani:Martani kan harin da Iran ta kai Isra'ila

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da taron gaggawa domin lalubo hanyoyin dakile fantsamar rikicin yankin Gabas ta Tsakiya da ke kara rincabewa, sakamakon hare-haren daukar fansa da ke zafafa tsakanin Iran da Isra'ila. Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Saeed Iravani, ya shaida wa kwamitin tsaron cewa kasar sa ta kai wa Isra'ila hare-haren makamai masu linzami kusan 200 kan Isra'ila a matsayin wata togaciya ta taka wa Isra'ilan birki daga tayar da wata tarzoma.

Yayin da shi kuma takwaransa na Isra'ila Michael Herzog ya bayyana lamarin a matsayin takalar fada. Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin daukar fansa, a gefe guda kuma shugaban Amurka Joe Biden ya nuna rashin goyon bayansa ga yunkurin da Isra'ila ke yi na farwa ma'ajiyar makamashin nukiliyar Iran, amma dai yana tare da Isra'ilan.