1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta kai sabbin hare hare a Beirut

Abdullahi Tanko Bala
November 1, 2024

Israila ta yi luguden wuta a yankin Dahiye da ke kudancin birnin Beirut inda ta lalata gidaje da dama sai dai babu dai rahoton hasarar rayuka.

Harin Isra'ila a yankin Dahiyeh na Beirut
Hoto: Hassan Ammar/AP Photo/picture alliance

A baya bayan nan Israila ta tsananta hare hare ta sama a arewa maso gabas da kuma kudancin Lebanon. Masu shiga tsakani na kokari domin samun yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon da kuma Gaza.

Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta ce mutane fiye da 2,800 suka rasa rayukansu yayin da wasu 13,000 kuma suka sami raunuka tun daga ranar 8 ga watan Oktoba lokacin da Hizbullah ta fara harba rokoki zuwa cikin Israila.

Yawan mutanen da suka rasu a yakin Israila da Hamas a Gaza ya haura mutum 43,000 yayín da harin da Hamas ta kai wa Israila na ranar 7 ga wata Oktoba ya hallaka 'yan Israila 1,200 yawancin su fararen hula ta kuma yi garkuwa da wasu mutanen 250