1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta kai sabbin hare-hare a Lebanon

March 8, 2026

Hukumomi a Lebanon na cewa, kasar ta fuskanci wasu hare-hare ta sama kan wani otel da ke tsakiyar birnin Beirut yayin da ake ci gaba da gwabza yaki a yankin Gabas ta Tsakiya.

Isra'ila ta kai sabbin hare-hare a Lebanon
Isra'ila ta kai sabbin hare-hare a LebanonHoto: Nidal Solh/AFP

Yayin da aka shiga mako na biyu na rikicin yakin Gabas ta Tsakiya, ma'aikatar lafiya ta kasar ta ce a kalla mutane takwas ne suka jikkata a harin da aka kai kan wani otel a birnin Beirut na Lebanon a safiyar wannan Lahadin. Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai harin ne kan kwamandojin dakarun na juyin-juya-halin Iran wato IRGC da ke Beirut din.

Karin bayani: Fafutukar sasanta rikicin Yankin Gabas ta Tsakiya

Rahotanni sun yi nuni da cewa, hare-haren na wannan safiyar sun shafi wata cibiyar mai da ke Tehran da ma wasu wurare a Iran. Sabbin farmakin na zuwa ne bayan da shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian ya nemi afuwar kasashe makwaftan Iran kan hare-harenta.