1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta kai sabbin hare-hare Lebanon

November 22, 2025

Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta tabbatar da mutuwar mutum daya a garin Zawtar al-Sharqiyah a kudancin kasar a wani harin da Isra'ila ta kai.

Isra'ila na ci gaba da kai hari Lebanon duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla
Isra'ila na ci gaba da kai hari Lebanon duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka kullaHoto: Mohammad Zaatari/AP Photo

Harin na zuwa ne duk da an shekara guda da kulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da kungiyar Hezbollah. A cikin sanarwar da ma'aikatar ta fitar, ta ce wani harin jirgi mara matuki da Isra'ila ta kai kudancin Shaqra ya jikkata mutum biyar. Sai dai Isra'ila har yanzu ba ta ce uffan ba kan hare-haren. Sai dai rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kashe wani mamba na kungiyar Hezbollah a yankin Froun. Ta kuma zargi Hezbolla da ci gaba da kai wa dakarunta hari.

Karin bayani: Isra'ila ta kai wani sabon hari a tsakiyar birnin Beirut na Lebanon

Lebanon na zargin Isra'ila da rashin mutunta yarjejeniyar bude wuta da aka cimma a watan Nuwambar bara. A cewar ma'aikatar lafiyar kasar, fiye da mutane 330 ne aka kashe a Lebanon yayin da wasu kusan 1,000 suka jikkata tun bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiyar.