1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta kai sabbin hare-hare Tehran

March 30, 2026

Rundunar sojin Isra'ila ta kai sabbin hare-hare Tehran babban birnin Iran, yayin da ita ma Iran din ta kai hari Kuwait da Saudiyya.

Isra'ila ta kai sabbin hare-hare Tehran
Isra'ila ta kai sabbin hare-hare TehranHoto: Ahmad Gharabli/AFP

Hare-haren na Isra'ila a Tehran na zuwa ne kwana guda bayan da Shugaba Trump na Amurka ya hakikance cewa za a iya cimma matsaya nan ba da jimawa ba. Itama Iran ta kadammar da sabbin hare-hare kan kasashen Kuwait da Saudiyya bayan hare-haren da aka kai kan wasu cibiyoyin lantarkinta a karshen mako, har ya haifar da zama cikin duhu a wasu sassan Tehran da kewaye.

Karin bayani:Iran ga Amurka: Kifi na ganinka mai jar koma 

A gefe guda kuma, Shugaba Trump ya ce yana son mallake man Iran tare da kwace tsibirin Kharg da Iran ke samun mai da take fitarwa. A lokacin da ake tattauna da shi da jaridar Financial Times, Trump ya ce babban abin da ya fi burge shi a yanzu shi ne kwace iko da man na Iran, sai dai a cewarsa wasu Amurkawa marasa kan gado na kalubalantarshi.