Isra'ila ta kai sabon hari a Gaza
August 14, 2014Rahotanni daga yankin Zirin Gaza na Falasdinu, sun tabbatar cewa jiragen yakin Isra'ila sun yi ruwan bama-bama a yankin arewacin Gaza, a cewar wadanda suka gane ma idanun su, da ma 'yan kungiyar Hamas: Hakan ya faru ne duk kuwa da cewa, an sanar da batun kara wa'adin tsagaita wutar da ya kare a ranar Laraba ya zuwa kwanaki biyar nan gaba daga wannan Alhamis. Sai dai ana ganin cewa da alama babu wadanda suka rasu cikin wannan sabon harin na Isra'ila.
Firaministan Isra'ila Benjamin Nethanyahu ne ya bai wa rundunar sojan kasar izinin kai wannan hari a matsayin mayar da martani kan wata roka da aka harba a cewar su daga yankin na arewacin Zirin na Gaza 'yan mintoci kalilan kafin lokacin cikar wa'adin tsagaita wutar, zargin da kungiyar Hamas ta karyata.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu