1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta kai wa Hezbollah hari tare da kashe-kashe a Gaza

Mouhamadou Awal Balarabe
October 20, 2024

Sojojin Isra'ila sun sanar da cewa sun kai hare-hare a wurare 175 a yankin Falasdinawa da kasar Lebanon a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, ciki har da ma'ajiyar makamai da wuraren harba rokoki na Hamas da Hezbollah.

Wasu sassan birnin Lebanon na ci gaba da shan luguden bama-bamai daga sojojin Isra'ila
Wasu sassan birnin Lebanon na ci gaba da shan luguden bama-bamai daga sojojin Isra'ilaHoto: Hussein Malla/AP/picture alliance

Sojojin Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a tungaye da dama na kungiyar Hezbollah a birnin Beirut da kudancin kasar Lebanon. Sannan suna ci gaba da kai farmaki a kan Hamas a Zirin Gaza, inda wani harin ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 70 a ranar Asabar, a cewar jami'an agajin gaggawa.  A yakin da suke yi da wadannan kungiyoyi da Iran ke mara wa baya, sojojin Isra'ila sun sanar da cewa sun kai hare-hare a wurare 175 a yankin Falasdinawa da kasar Lebanon a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, ciki har da ma'ajiyar makamai da wuraren harba rokoki na Hamas da Hezbollah.

Karin bayani: 

Isra'ila ta ce wannan hafsnta sojanta ya mutu a farmakin, yayin da a nata bangaren, kungiyar Hezbollah ta dauki alhakin hare-haren rokoki da aka kai birnin Haifa, da wani sansanin soji da ke kusa da Safed da ke arewacin Isra'ila, da kuma kan wasu sojojin Isra'ila a kudancin Lebanon.