1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta kai wani sabon hari a tsakiyar Beirut

November 23, 2024

Isra'ila ta kai wani farmaki ta sama a tsakiyar birnin Beruit na kasar Lebanon, yayin da take ci gaba da matsa kaimin kai hare-hare kan kungiyar Hezbollah.

Hoto: -/AFP

A kalla mutane hudu ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da wasu 23 suka jikkata a harin da Isra'ilar ta kai Basta da ke kusa da birnin Beirut. Kamfanin dillacin labaran Lebanon ya kuma ruwaito cewa,harin ya yi sanadin rushewar wani gini mai hawa takwas, yayin da bangarorin wasun gine-ginen da ke kusa suka lalace. Wannan dai shi ne karo na hudu da Isra'ila ta kai hari a wannan makon a tsakiyar birnin Beirut.

Karin bayani: Isra'ila ta kai sabbin hare hare a Beirut

Alkalumma sun yi nuni da cewa, kimanin mutane 3,700 ne aka kashe a Lebanon tun bayan barkewar rikici a tsakanin Isra'ila da mayakan Hezbollaha cewar ma'aikatar lafiya ta kasar.