1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta kai wasu sabbin hare-hare a Gaza

Binta Aliyu Zurmi
January 31, 2026

Akalla mutane 29 ne sabbin hare-haren Isra'ila a Gaza ya hallaka a wannan rana ta Asabar. Adadin dake zama mafi girma tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a watan Oktoban bara.

USA Palm Beach 2025 | Benjamin Netanjahu und Donald Trump bei Pressekonferenz in Mar-a-Lago
Hoto: Joe Raedle/AFP/Getty Images

Sabbin hare-haren na zuwa ne kwana guda bayan da Isra'ila ta zargi Hamas da saba ka'idojin tsagaita bude wuta.

Har ila yau jerin hare-haren sun zo ne gabanin cika ranar da Isra'ila ta yi alkawarin bude mashigar Rafah da ke kan iyaka da Masar, wani muhimmin mataki a yarjejeniyar da aka cimma a bara a matsayin hanyar kawo karshen yakin.

Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta bayyana cewar sama da Falasdinawa 500 ne hare-haren Isra'ila suka hallaka tun bayan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a ranar 10 ga watan Oktoba shekarar 2025.

Karin Bayani: Isra'ila ta binne gawar karshe da aka dawar daga Gaza