SiyasaGabas ta Tsakiya
Isra'ila ta karbe iko da Rafah da ke iyakar Masar
May 7, 2024![](https://static.dw.com/image/69008326_800.webp)
Talla
Gidan radiyon sojin Isra'ila ne ya sanar da daukar wannan mataki na karbe iko da kan yankin na Rafah da ke kan iyakar Gaza da Masar.
Karin bayani:Amurka ta jaddada adawa da kutsen Isra'ila a Rafah
Kodayake sojojin Isra'ila sun bayyana cewa nan gaba kadan a wannan rana ta talata zasu fitar da sanarwa kan daukar wannan mataki.
Karin bayani: Isra'ila ta kaddamar da sabbin hare-hare a zirin Gaza
Sannan gwamnati Isra'ila ta yi watsi da yarjejeniyar tsagaita wutar da ta ce bai kumshi muhimman abubuwan da take bukata ba, duk da cewa a daya bangaren Hamas ta amince da tayin tsagaita bude wuta.