1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Netanyahu ya cika alkwarin karbe gabar kogin Jordan

Ramatu Garba Baba
September 15, 2019

Isra'ila ta amince da kudurin dokar da zai bata damar mayar da wani yanki na gabar yamma da Kogin Jordan nata, wanda ke nufin za ta mamaye yankin da dubban Falisdinawa ke zaune.

Israel, Jerusalem: Netanjahu hält Pressekonferenz zu Atompolitik Irans
Hoto: Reuters/R. Zvulun

A wannan Lahadin ne, Firai ministan ya rattaba hannu kan kudurin dokar a gabanin gudanar da zaben da ya ke fuskantar kalubale daga abokin takararsa. Netanyahu ya sha suka a makon da ya gabata bayan da ya dauki wannan alkawarin, da ya ce zai cika muddun aka sake zabensa, sai dai ya zo wa da dama da mamaki yadda ya yi hanzarin cika alkawarin kwanaki biyu kafin ma a gudanar da zaben. Kasashen duniya sun baiyana fargabar cewa, matakin Netanyahun zai iya rusa shirin samar da maslaha a tsakanin Isra'ilan da Falisdinu da aka dade ana fatan ganin an yi.     
 

.