1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta kashe akalla mutum 22 a zirin Gaza

December 23, 2024

Sabon harin da sojojin Isra'ila suka kaddamar ya halaka yara da kuma masu addu'o'in Kirsimeti.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benjamin NetanyahuHoto: Uncredited/Israeli Government Press Office/AP/dpa/picture alliance

Isra'ila ta kashe akalla mutum 22 a zirin Gaza cikinsu har da yara biyar a cewar jami'an kiwon lafiyar Falasdinawa.

Wannan harin na zuwa ne a daidai lokacin da wasu Kiristoci a zirin suka fara gudanar da addu'o'in Kirsimetin 2024.

A wani harin na daban, sojojin na Isra'ila sun far wa jama'a tare da kashe mutum biyu a cikin wata mota a kudancin garin al-Mawasi da kuma wani harin a arewacin Gaza.

Isra'ila ta kai jerin farmaki a Yamen

Kusan Falasdinawa miliyan biyu ne ke neman kare kansu daga sanyi a yayin da Isra'ila ke ci gaba da kaddamar da hare-hare a zirin.

Isra'ila ta aikata 'kisan kare dangi' a Gaza - Amnesty International

 Farashin barguna da itace da kuma tufafi ya yi tashin gwauron zabi saboda yanayin sanyi da ake fama da shi.