Isra'ila ta kashe dan Al Jazeera kan zargin shiga Hamas
August 11, 2025
Rundunar sojin Isra'ila ta sanar da halaka ma'aikacin gidan Talabijin na Al Jazeera da ta zarga da zama dan kungiyar Hamas, mai suna Anas Al Sharif, mai shekaru 28 da haihuwa, bayan harin da ta kai kan wani tanti da ke kusa da asibitin Al-Shifa a gabashin Gaza ranar Lahadi.
Sauran 'yan jaridar da harin ya kashe sun hada da Mohammed Qreiqeh da Ibrahim Zaher da Mohammed Noufal, wanda Al Jazeera ta yi tir da harin.
Gabanin mutuwar Anas Al Sharif, sai da ya bar wasiyyar da ya ce a wallafa bayan ya mutu, da ke kunshe da sakon cewa yana aiki bisa gaskiya da adalci babu tsoro babu ja da baya.
A cikin watan Yulin 2025 wasu kungiyoyin kare hakkin 'yan jarida suka sanar da cewa rayuwar Anas Al Sharif na cikin hadari, sakamakon yadda ya yi kaurin suna wajen aika rahotannin hare-haren da Isra'ila ke kai wa zirin Gaza.
A gefe guda firaministan Australia Anthony Albanese ya sanar da cewa kasarsa za ta amince da wanzuwar Falasdinu a matsayin kasa 'yantacciya, a lokacin babban taron zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 80 a watan Satumba na 2025.
Mr Albanese ya tabbatar da wannan kuduri ne ranar Litinin, yayin taron manema labarai a Canberra babban birnin kasar, yana mai jaddada cewa samar da kasashe biyu 'yantattu ne mafita, kan rikicin yankin Gabas ta Tsakiya da ya ki ci ya ki cinyewa tsawon shekaru.
Sanarwar ta Australia na zuwa ne bayan da kasashen Burtaniya da Faransa da kuma Canada suka bi sahun sauran kasashen duniya da suka amince da ayyana Falasdinu a matsayin kasa mai 'yancin cin gashin kai.
Kuma kasashe 150 ne yanzu haka ra'ayinsu ya zo daya, wajen aminta da wannan kuduri, wanda Amurka mai karfin ikon hawa kujerar na ki ke nuna tirjiya a kai.
A ranar Juma'a firaministan Isra'ila Benjamin Nertanyahu ya bayyana shirinsa na kwace ikon Gaza da karfin tuwo, wanda kasashen duniya da dama suka bukaci ya janye muradinsa.
Haka zalika New Zealand na duba yiwuwar amincewa da Falasdinu a matsayin kasa mai 'yancin cin gashin kai, kamar yadda ministan harkokin wajen kasar Winston Peters ya sanar ranar Litinin.
Firaministan kasar Christopher Luxon zai sanar da cimma matsayar, gabanin babban taron zauren Majalisar Dinkin Duniya mai zuwa, da zarar ya samu sahalewar majalisar zartarwarsa, in ji Mr Peters.