Sojojin Isra'ila sun kai hari a Nablus
February 22, 2023Talla
Sojojin Isra'ila sun kashe Falasdinawa shida kana suka raunana wasu fiye da 50.Kusan shekara guda ke'nan da dakarun Isra'ilar ke matsa kaimi da hare-hare a matsayin na yaki da ta'addanci a yankin arewacin Gabar Kogin Jordan,musamman ma a garuruwan Nablus da Jenin,tungar kungiyoyin Falasdinawa masu dauke da makamai.