1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta kashe sama da mutane 300 a Lebanon

April 9, 2026

Ma’aikatar lafiya ta Lebanon ta sanar cewa harbin saman da Isra’ila ta kai a fadin ƙasar yayi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 300 tare da jikkata akalla 1,150 ciki har da jami'an kiyaye zaman lafiya na MDD.

Yadda ake binne gawarwaki a Lebanon
Yadda ake binne gawarwaki a LebanonHoto: Kawnat Haju/AFP

A cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta kara da cewa jimillar adadin wadanda suka mutu tun farkon rikicin tsakanin Isra’ila da ƙungiyar Hezbollah mai goyon bayan Iran a ranar 2 ga Maris ta kai 1,888 da jikkata mutane dubu 6 da 92.

Ma’aikatar ta yi gargadi cewa adadin mutanen da suka mutu na iya ƙaruwa yayin da ake ci gaba da ayyukan bincike da gwajin DNA na gawawwakin da aka kai asibitoci. Gamayyar kasashe sama da 60 da suka girka dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun yi Allah wadai da kashe jami'ai uku a yakin Lebanon.

Kasashen da suka hada da Indonesiya, da Faransa, da birtaniya, da China da Turkey da kuma Rasha, sun yi kira ga Isra'ila da Hezbollah su dakatar da rikicin.