1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta kashe wani babban kwamandan Hezbollah a Beirut

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
September 24, 2024

Dubban mutane ne dai ke kaurace wa yankin kudancin Lebanon, biyo bayan rincabewar rikicin

Hoto: FADEL ITANI /AFP

Isra'ila ta sanar kashe wani babban kwamandan Hezbollah Ibrahim Kobeisi, a harin makami mai linzami da na roka da dakarunta suka kai Beirut babban birnin Lebanon a Talatar nan. Isra'ila ta ce tun a cikin shekarun 1980 Ibrahim Kobeisi ya shiga kungiyar Hezbullah, kuma shi ne ya kitsa yadda aka kama sojojinta uku aka kashe a shekarar 2000.

Karin bayani:Isra'ila tana ci gaba da kai farmaki Lebanon

Dubban mutane ne dai ke kaurace wa yankin kudancin Lebanon, biyo bayan rincabewar rikicin, inda suke kwana a makarantu da sansanonin wucin-gadi da aka kafa, domin tsere wa yakin.

Karin bayani:Isra'ila ta kai hare-hare kan kungiyar Hezbullah a Lebanon

Ofishin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a Lebanon ya ce daga cikin wadanda harin Beirut na ranar Litinin ya halaka har da ma'aikaciyarsa da kuma 'danta, yayin da mai gidanta da daya daga cikin 'ya'yanta suka samu raunuka, sai kuma wata mai kula da gyare-gyaren ofis din da itama ta rasa ranta.