1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

Isra'Ila ta kori manyan sojoji kan harin Hamas

Abdullahi Tanko Bala
November 24, 2025

Isra'ila ta fara daukar mataki kan manyan sojoji da jami'an tsaro bayan wani bincike da ya ce sojoin sun gaza wajen hana aukuwar harin da Hamas ta kai na ranar 7 ga watan Oktoban 2023

Wurin da Hamas ta kai hari Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, 2023
Wurin da Hamas ta kai hari Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, 2023Hoto: Ariel Schalit/AP Photo/picture alliance

Babban hafsan sojin Isra'ila Laftanar Janar Eyal Zamir ya sanar da sallamar wasu manyan jami'an sojin kasar tare da ladabtar da wasu game da gazawar su wajen hana aukuwar harin ranar 7 ga watan Oktoban 2023 da Hamas ta kai.

A cikin wata sanarwa rundunar sojin ta tabbatar da sallamar sojojin tana mai cewa ba za a sake daukar su aikin soji ba.

Wadanda aka sallama daga aiki sun hada da tsoffin shugabannin hukumar leken asiri da shugabannin sashen gudanarwa na sojin wadanda dukkaninsu sun yi ritaya a baya amma kuma suna ci gaba da zama kan mukamansu.

Matakin ladabtarwar ya biyo bayan matsin lamba daga al'ummar kasar da ke bukatar a gudanar da bincike. Gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu kawo yanzu ba ta kaddamar da binciken harin ba.

Dubban jama'a sun bi sahun gangamin 'yan adawa a birnin Tel Aviv suna kira a kafa kwamitin bincike na kasa.