1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta kutsa cikin Deir al-Balah na Gaza ta kasa

July 21, 2025

Mazauna garin sun ce tun a ranar Lahadi Isra'ila ta basu umarnin ficewa daga gidajensu.

Wannan shi ne karon farko da sojojin Isra'ila suka shiga garin ta kasa
Wannan shi ne karon farko da sojojin Isra'ila suka shiga garin ta kasaHoto: Abdel Kareem Hana/AP/picture alliance

A karon farko tun bayan fara yakin Gaza sojojin Isra'ila sun fara shiga cikin garin Deir al-Balah ta kasa, kamar yadda shaidu suka bayyana a ranar Litinin.

Mazauna yankin sun ce sojojin Isra'ila sun kwace gine-gine a kudu maso yammacin birnin da ke tsakiyar Gaza kuma sun saka masu harbi daga nesa a kan rufin gine-gine.

Gomman Falasdinawa sun mutu wajen jiran kayan agaji

Dakarun Isra'ila ba su fitar da wata sanarwa ba dangane da wannan kutsen.

A ranar Lahadi, sojojin sun umarci mutane su fice daga wasu unguwanni a kudu maso yammacin birnin kuma mazauna sun ce sun bar gidajensu da sassafe ranar Litinin.

Merz na Jamus ya caccaki Isra'ila bisa rikicin Gaza

‘Yan jaridar da ke aiki a Falasdinu sun shaida wa BBC cewa, tankokin Isra'ila sun kutsa yankin, tare da kaddamar da hare-haren sama da na artilari.