1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta lalata hanyar da al'ummar Lebanon ke shiga Syria

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim MAB
October 4, 2024

Mai magana da yawun dakarun tsaron Isra'ila Avichay Adraee, ya ce 'yan kungiyar Hezbollah ne ke amfani da hanyar wajen safarar makamai cikin Lebanon

Ire-iren motocin da Isra'ila ke jibgewa a kan iyaka
Ire-iren motocin da Isra'ila ke jibgewa a kan iyakaHoto: Menahem Kahana/AFP/Getty Images

Isra'ila ta lalata babbar hanyar da dubban al'ummar Lebanon ke bi don shiga Syria, bayan ruwan bama-baman da ta yi wa hanyar da safiyar Juma'ar nan, kamar yadda ministan sufurin Lebanon Ali Hamieh ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters. Mr Hamieh ya ce luguden wutar da dakarun Isra'ila suka yi wa hanyar Masnaa da ke kusa da iyakarta da Syria, ya haddasa wani wawakeken ramin da ya hana mutane wucewa. Sai dai mai magana da yawun dakarun tsaron Isra'ila Avichay Adraee, ya sanar da cewa 'yan kungiyar Hezbullah ne ke amfani da hanyar wajen safarar makamai cikin Lebanon, don haka ba za su bari a yi mu su sakiyar da ba ruwa ba, kamar yadda ya wallafa a shafina na X.

Karin bayani:Isra'ila ta kai munanan hare-hare a tsakiyar birnin Beirut

A  karon farko cikin kusan shekaru biyar, jagoran addini na kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei, zai jagoranci sallar Juma'a a babban masallacin kasar na Imam Khomeini da ke Tehran babban birnin kasar, inda zai gabatar da huduba, a daidai lokacin da Iran ke fama da rikici da Isra'ila. Hakan na zuwa ne kwanaki uku gabanin cika shekara guda cur da barkewar rikicin Gaza, bayan da Hamas ta kai wa Isra'ila hari ranar 7 ga watan Oktoban bara.

Karin bayani:Martani kan harin da Iran ta kai Isra'ila

Rabon da ya jagoranci sallar Juma'a tun cikin watan Janairun shekarar 2020, lokacin da Iran ta harba makamai masu linzami zuwa sananin sojin Amurka da ke Iraqi, a matsayin martanin kisan da Amurkan ta yi wa babban kwamandan dakarun musamman na Revolutionary Guards Qasem Soleimani.