Hamas ta cilla wa Isra'ila dubban makaman roka
October 7, 2023A Gabas ta Tsakiya, sabon tashin hankali ya barke a yankin Zirin Gaza biyo bayan wasu jerin hare-hare na ba zata da kungiyar Hamas ta kai wa Isra'ila, inda ta cilla mata dubban makaman rokoki.
A cikin wani sakon bidiyo da ya aike jim kadan bayan hare-haren, firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahou ya ce suna cikin yaki inda ya sha alwashin murkushe 'yan kungiyar ta Hamas.
Barkewar sabon tashin hankalin na zuwa ne a daidai lokacin da ake shagulgulan ranar karshe ta bukukuwan Yahudawa wanda ke samun halartar dumbin masu yawon buda ido.
A cikin wani sako na murya da gidan talabijin mallakar Hamas ya watsa an jiyo shugaban kwamandojin kungiyar na cewa sun harba wa Isra'ila dubban makaman roka, abin da ya kira da sunan farmaki da suka kaddamar kan kasar, a wani mataki na mayra da martani da farmakin da suka yi zargin Isra'ila na kai wa masalalcin Alqasa.
Tuni dai kasashen duniya suka fara bayyana fargaba tare da yin tir da wannan sabon tashin hankali da ya barke a tsakanin bangarorin biyu.
Shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta yi Allah wadai da hare-haren da ta alakanta da na ta'addanci tana mai cewa Isra'ila na da 'yancin kare kanta daga wannan abin da ta siffanta da aika-aika.
A share daya kuma Rasha ta kira bangarorin biyu da su kai zucciya nesa, yayin da shugaba Erdogan na Turkiyya ya bukaci Falasdinawa da su nemi 'yancinsu cikin ruwan sanyi amma su guji abin da zai iya haifar da tashin hankalin da ba a san karshensa ba.