Isra'ila ta sake aika dakaru zuwa Siriya
May 4, 2025
Talla
Wannan wani shiri ne nata a cewar rundunar, da ke nufin dakatar da sojojin Siriya daga shiga kudancin da ke dauke da matsugunan 'yan kabilar Druze marasa rinjaye.
Sojojin na Isra'ila dai ba su bayar da adadin mayakan da aka aike da su zuwa kudancin na Siriya ba.
Gwmanatin Firaminista Benjamin Netanyahu dai ta tsaurara sintirin soji a kudancin Syria ne, tun bayan kawo karshen gwamnatin Bashar al-Assad a cikin watan Disamba.
Ko a ranar Juma'a ma dai Isara'ilar ta kaddamar da wasu hare-are ta sama a kusa da fadar shugaban kasar Siriya da ke a Damascus babban birnin kasar.
Hare-haren dai na zuwa ne bayan kalaman da Netanyahu ya yi na cewar Isra'ila za ta tsoma hannunta, muddin dai gwamnatin Siriya ta yanzu ta ki kare tsirarun 'yan kabilar Druze.