Isra'ila ta sake kashe Falasdinawa
April 28, 2018Rahotannin da ke fitowa daga zirin Gaza, na cewa sojojin Isra'ila sun kashe akalla falasdinawa hdu ciki har da wani dan shekara 15 Azzam Oweida. Bayanan sun ce akwai akalla mutum 900 wadanda ke zanga-zanga a jiya Juma'a, da suka jikkata. Ma'aikatar lafiya ta yankin Gaza, ta ce wadanda ke kwance a asibiti sun zarta tunani da ma iyawar likitocin da ke yi masu maganai, sakamakon raunukan harbi da bindiga da kuma shakar iska mai guba da suka yi.
Rundunar sojin Isra'ila dai ta ce dakarunta sun kare iyakarsu ne daga barazanar da daruruwan masu zanga-zanga ke yi masu. Sun kuma yi zargin falasdinawan da amfani da boma-boma da kuma gurnet-gurnet, abin kuma da ya tilasta sojojin buda masu wuta.
A ranar 30 ga watan jiya ne dai falasdinawan suka sabonta jerin zanga-zangar neman komawa yankunansu na asali da Isra'ila ta mamaye, shekaru 70 din da suka gabata. Sai dai fa Isra'ilar, ta musanta hakan tare da gargadin abokan nasu na jayayya, da su kiyaye haduwa a kan shingen da ke tsakanin bangarorin biyu.