Israila ta soki binciken FBI kan Abu Akleh
November 15, 2022Israila ta ce binciken da hukumar FBI ta Amirka tace za ta yi kan kisan Ba Amurkiya kuma 'yar asalin Falasdinu Shireen Abu Akleh kuskure ne kuma Israila ba za ta bada hadin kai ga binciken ba.
Abu Akleh 'yar jaridar Aljazeera ta rasa ranta ne yayin da ta ke daukar rahotoanni yayin wani farmaki da sojojin Israila suka kai yankin gabar yamma a ranar 11 ga watan Mayu.
A ranar 5 ga watan Satumba Israila ta amince cewa akwai yiwuwar daya daga cikin sojojinta ya harbi Abu Akleh bisa kuskure. Ministan tsaron na Israila Benny Gantz yace Israila ba za ta bada hadin kai ga wani bincike daga waje ba.
Iyalan 'yar jaridar ta Aljazeera Shireen Abu Akleh a wata sanarwa da suka fitar sun yabawa matakin Amirka na binciken musababbin kisanta wanda suka ce suna fatan samun bincike na adalci.