Isra'ila ta tilasta wa tawagar Flotilla komawa gida
October 2, 2025
Isra'ila ta ce za ta mayar da 'yan gwagwarmayar nan na Falasdinu da ke cikin ayarin jiragen ruwan Flotilla wadanda suka yi yunkurin shiga Gaza don kai kayan agaji.
Ayarin jiragen ruwan da ake kira Global Sumud Flotilla su kimanin 45 ne, kuma sun fara tafiya ne a watan da ya gabata don shiga Gaza.
Amurka ta gabatar da sabon shiri kan Gaza
Daga cikin mutanen har da mai fafutukar sauyin yanayi daga Sweden, Greta Thunberg kuma sun sha alwashin kai kayan abinci da magunguna a yankin da Majalisar Dinkin Duniya ta ce yunwa na addabar al’umma.
Rundunar sojan ruwan Isra’ila ta kama jirgen a cikin teku, bayan ta yi gargadi ga masu fafutuka da kada su shiga yankin ruwan da ta haramta a shiga.
Trump ya nuna alamar samun maslaha a Gabas ta Tsakiya
Ministan Harkokin Wajen Girka, George Gerapetritis ya ce an kama jirage kusan 39 daga cikin guda 45 kuma suna kan hanyarsu zuwa tashar jiragen ruwa ta Ashdod a Isra’ila.