1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta tsananta kai hare-hare a Iran

June 15, 2025

Isra'ila ta ci gaba da hare-harenta zuwa Iran tare da barazanar da amfani sosai bayan wasu makaman Iran sun fada cikin kasar. Rayuka dai na salwanta a kwanaki uku da fara kai wa juna hare-hare.

Hare-haren Isra'ila a cikin kasar Iran
Hare-haren Isra'ila a cikin kasar IranHoto: Ahmad Hatefi/UPI Photo/IMAGO

Isra'ila ta ci gaba da kai hare-harenta ta sama a fadin Iran tare da barazanar yin amfani ka karfi fiye da kima, bayan wasu makaman Iran sun tsallaka zuwaa Isra'ila inda suka fada a kan gine-gine a tsakiyar kasar.

An dai kai ga soke tattaunawar da aka shirya yi a yau Lahadi a kan shirin nukiliyar Iran, wanda zai iya zama hanyar samun sulhu.

Hare-haren Isra'ila cikin kwanaki uku, sun yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 406 a Iran tare da raunata wasu 654, a cewar wata kungiya mai rajin kare hakkin dan Adam da ke Washington, wadda ta dade tana bibiyar al'amuran kasar.

A takaice, rikicin ya shiga wani sabon mataki na tashin hankali mai tsanani, inda hare-hare ke kara ta'azzara tsakanin Isra'ila da Iran, yayin da kasashen duniya ke kira ga zaman lafiya da tattaunawa.

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW