1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Isra'ila ta umurci a kwashe fararen hula daga garin Rafah

Binta Aliyu Zurmi
February 10, 2024

Firaministan Isra'ila Benjamin Nethanyahu ya umurci dakarun sojinsa da ke ci gaba da kutsa wa a Gaza da su kwashe fararen hula da ke neman mafaka a garin Rafah mai iyaka da kasar Masar.

Gazastreifen Rafah | Improvisierte Notunterkünfte
Hoto: Abed Zagout/Anadolu(picture alliance

Sama da 'yan gudun hijirar Gaza 1,300,000 ne ke tsugunne a Rafah bayan tserewa daga matsugunnensu.

Kiran a kwashe wadannan al'umma da Nethanyahu ya yi ya janyo kakausar suka daga kungiyoyin kare hakkin al'umma da ma Amurka.

Amurka dai tuni ta gargadi dakarun na Isra'ila a kan hadarin da ke tattare da shirin kai hari a wannan yanki, a cewarsu zai iya zama bala'i mafi muni da za a gani a wannan yakin da suke yi da Hamas.

Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana cewa Isra'ila ta wuce gona da iri a ramuwar harin ranar 7 ga watan Oktoba da aka kai mata.